Hello Everyone welcome to AFRI-TUNES WEEK 172 a song cover by @santos99 from house Bible hymm title Akwai sunana Mai dadi Wanda ba mai kamansa ( Take the precious name) this is a life changing song.
Song lyrics
- Akwai sunan nan mai daɗi wanda ba mai kamarsa,
Wato sunan Ubangiji, begen dukan Masu Bi.
KORUS
Sunan nan, Yesu ne, sunansa da daɗin ji,
Sunan nan, Yesu ne, begen dukan Masu Bi.
- Tun da na ji sunan Yesu, murna na ke yi sosai.
Wurinsa na sami ceto, gafara da kwanciyar rai.
Korus
- Cikin sunan nan mai girma, a ke samun ceto fa,
Cikinsa a ke sujada, cikinsa a ke addu'a.
Korus
- Sunan nan ya buɗe ƙofa, zuwa Allah Ubansa,
Gama ban da sunan Yesu, Allah ba za ya ji mu ba.
Korus
Source